Wani Fasto ya mutu bayan da wani ginin Cocin Dunamis da ke ofishin Ward North Bank a Makurdi, babban birnin jihar Benue ya ruguje da sanyin safiyar ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.
Rahotanni sun bayyana cewa limamin cocin tare da wasu mutane na gudanar da addu'o'i a ginin cocin a lokacin da ya ruguje. Wasu mutane ukun da ke harabar cocin sun tsere da ransu.
Gine-ginen gidaje da kayayyakin wutar lantarki da ke kewayen ginin sun ruguje.
Kawo yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.
DAGA ISYAKU.COM