Rundunar Hunters Council of Nigeria reshen jihar Kebbi tare da ƙungiyoyin sa kai don tsaro sun cafke wani matashi yayin da suka fatattaki wasu matasa da suka cire surken wayar lantarki a Birnin Kebbi.
Kwamandan Rundunar na jihar Kebbi Malam Musa Rambo ya shaida wa manema labarai yayin mika surken wayoin lantarki da suka kama ga hukumar Kebbi Development Authority KUDA ta hannun Manajan hujumar, a harabar hukumar da ke Birnin kebbi ranar Talata 3, Oktoba, 2023.
Rambo ya ce sun kama wani mai suna Chukwudi dauke da surken wayar lantarki da misalin karfe 3 na dare a kusa da Masallacin Malam Abbas da ke unguwar rafin Atiku a garin Birnin kebbi.
Ya ce sun mika wanda aka kama ga hukumar Yan sanda don gudanar da bincike.
Kazalika Rambo ya ce sun yi nassarar kwace surken wayar lantarki bayan samarin da suka gino wayar a Unguwar Kofar Kola sun yar da wayar suka gudu bayan sun gano jami'ai tafe.
Ya ce za su ci gaba da gudanar da aikin kama masu satar wayoyin lantarkin a garin Birnin kebbi yayin da ya bukaci jama'a su bayar da hadin kai domin taimakawa wajen samun nassara.
DAGA ISYAKU.COM