Kayya: An kama korarren jami'in tsaro bayan ya tafka satar dukiyar jama'a


Rundunar ‘yan sandan jihar Abia, ta ce ta cafke wani jami’in ‘yan sanda da aka kora, Francis William, a lokacin da yake yunkurin satar tiransifoma na kamfanin wutar lantarki na Aba da ke National High School Port-Harcourt, Aba.


 Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Kenechukwu Onwuemelie ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023, yayin da yake zantawa da manema labarai a Umuahia kan ayyuka da nasarorin da rundunar ta samu daga watan Yuli zuwa Satumba.


 CP Onwuemelie, wanda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Maureen Chinaka ya wakilta, ya ce jami’an tsaro daga hedikwatar ‘yan sanda na Ndiegoro, Aba, sun kama William, mai shekaru 34, da misalin karfe 6 na yammacin ranar 11 ga watan Satumba.


 Ya ce an kama mutumin ne sanye da tufafin ‘yan sanda, da hular fes cap, kuma yana rike da katin shaidar ‘yan sanda na bogi.


 “An kama shi, kuma an kwato dukiyar da ya sace, an gurfanar da shi a gaban kotu, kuma an tsare wanda ake zargin a gidan yari,” inji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN