Wasu ’yan daba sun kai hari kan wasu ‘yan sanda biyar da suka yi yunkurin ceto wani mutum da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a yankin Dei Dei da ke babban birnin tarayya.
An tattaro cewa ‘yan sandan da ke aiki da sashin ‘yan sanda na Gwagwa, sun je ceto mutumin da aka bayyana sunansa da Mubarak wanda ’yan daban suka kusa halaka shi a ranar Alhamis, 5 ga Oktoba, 2023.
A cewar Punch, wani mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba ya yi zargin bacewar mazakutarsa bayan ya yi musabaha da Mubarak.
Wani mazaunin yankin da bai so a ambaci sunansa ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa ‘yan daban sun kewaye wanda ake zargin tare da lakada masa duka cewa sai ya mayar wa mutumin da mazakutarsa.
Ya ce zuwan ‘yan sandan ya kara dagula lamarin ganin yadda ’yan daban maimakon su saki wanda ake zargin, sai suka far wa ‘yan sandan tare da lalata motarsu.
Kakakin hukumar Yan sandan Birnin Abuja SP Josephine Adeh ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an kama mutane 14 dangane da lamarin.
DAGA ISYAKU.COM