Lamarin ya faru ne da yammacin Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023, a unguwar Libbo, a kauyen Kate-Gamji.
Mutumin mai suna Ali Denham, an ce ya fara kashe mutanen ne ba dalili.
Lamarin ya fusata wasu matasa a kauyen suka kewaye mutumin, suka kwace masa makamai, suka yi masa duka har lahira.
"Ali Denham, wani mutum mai tabin hankali ya kashe mutane guda tara a kauyen sannan kuma fusatattun matasan unguwar sun kashe shi. Hakan ya faru ne a ranar Laraba a unguwar Sheleng," wata majiya ta shaida wa Sahara Reporters.
Wata majiyar ta kara da cewa, “Yana rike da wuka kuma duk wanda ya zo gurinsa ciki har da wata tsohuwa mace da tsoho namiji ya caka masu wukar. Ya tabbatar da cewa wanda ya daba masa wuka ya mutu kafin ya koma wurin wani.”
An yi jana’izar gawarwakin wadanda suka mutu a yammacin ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.
An kuma tattaro cewa ‘yan uwan mai tabin hankalin sun gudu daga cikin al’umma bayan samun labarin kashe-kashe da dan uwansu ya yi shi kuma aka kashe shi.
DAGA ISYAKU.COM