Rundunar Æ´an sanda reshen jihar Gombe ta cafke wani matashin yaro É—an shekara 18, Mustapha Adamu Isah, wanda aka fi sani da Abbati, bisa zargin kashe wata mata. Legit Hausa ya wallafa.
The Nation ta ce Ƴan sanda sun kama Abbati, wanda ake zargi da halaka Hajiya Aishatu Abdullahi wacce ake kira da Damori a Unguwar Jekadafari Quarters da ke cikin Gombe.
Mai magana da yawun rundunar Æ´an sandan jihar, ASP Mahid Mua’zu, shi ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wanda ake zargin a hedkwatar Æ´an sanda ranar Jumu'a.
Ya ce ranar Jumu'a 20 ga watan Oktoba, Æ´an sandan Caji Ofis É—in Pantami suka samu korafi daga É—an matar cewa wani makashi da bai gane ko waye ba ya yi wa mahaifiyarsa yankan rago.
Ya ce:
"Nan take jami'an Caji Ofis a Pantami suka kai É—auki wurin, suka tarad da matar Aishatu Abdullahi, kwance cikin jini, suka É—auke ta zuwa Asibitin koyarwa na Gombe inda aka tabbatar ta rasu."
Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa an kama Abbati ranar 22 ga watan Oktoba, 2023 bisa zargin hannu a kisan matar bayan samun sahihan bayanan sirri daga tawagar bincike.
A cewarsa, a yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga dakin Aishatu Abdullahi ne domin neman sufanarsa da ta kwace.
Wanda ake zargin ya kuma ambaci abokinsa, Idris Abubakar Danjauro, mai shekaru 17, wanda ya ce ya zo É—akin ya tama shi aikata wannan É—anyen aikin.
Sai dai Idris, wanda aka kama daga baya, ya musanta cewa bai san wanda ya kashe matar ba a lokacin da bincike ya biyo ta kansa, Tribune ta rahoto.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa Aishatu ta dawo daga makwabta, ta same shi a dakinta, ta tuhume shi tare da umartan ya fice mata daga É—aki amma ya ki fita."
"Wanda hakan ya sa ya afka mata, ya shake ta, ya kashe ta da wuka, ya tsere ta bayan gida zuwa inda ba a sani ba."
- ASP Mahid Muazu.