Israila ta kashe fiye da bayin Allah 500 da ke kwance a Asibiti a Gaza


A halin yanzu, suka kurum sojojin kasar Israila su ke sha a sakamakon wani mummunan hari da aka kai a asibitin Al-Ahli a Gaza. Legit ya wallafa.

Wannan asibiti ya na cikin tsofaffin asibitocin da kiristoci su ka kafa a yankin, Al Jazeera ta ce mutane sama da 500 bam ya hallaka a jiya.

Wani mutumi da aka yi hira da shi, ya shaidawa duniya yadda ake yi masu ruwan bama-bamai, ana kashe mutane a sakamakon harin Hamas.

A cewarsa, kowa ya na cikin dar-dar a zirin Gaza, ya kara da cewa ya na jin karan tashin bam a wajen gidansa, kullum abin ya na kara muni.

Khamis Elessi wanda fitaccen Likita ne a kasar Falasdin, ya tabbatar da wannan hari a yammacin Talata, ya ce roka ta hallaka mutane barkatai.

Ana zargin dakarun Israila ba su kyale har wuraren da fararen hula da masu jinya su ke ba, abin da musulmai da sauran al'umma su ke tir da shi.

Hakan ta so zo dole aka ji shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres a kasar Sin ya na sukar hare-haren da ake kai wa mutanen Gaza.

Guterres ya ce ta’adin Hamas bai ba Israila lasisin kashe wadanda babu ruwansu ba.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN