An gano asusun Banki sama da 570 da tsohon Gwamnan PDP ya boye kafin ya sauka mulki a Arewa


Gwamnatin jihar Benue ta zargi tsohuwar gwamnatin da ta shude ta tsohon gwamna Samuel Ortom na PDP da yin amfanu da asusu 600. Legit ya wallafa.

Gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Hyacinth Alia na APC ta caccaki Ortom ta ɓoye bayanan asusun banki sama da 570, inda ya nuna 25 kacal sa'ilin miƙa mulki.

Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafin kuɗi na jihar, Michael Oglegba, ne ya faɗi haka yayin da tawagar ƙungiyar 'yan jarida (NUJ) ta kai masa ziyara a Ofis ranar Talata a Makurɗi.

Ya ce bisa wannan dalili ne mai girma Gwamna Alia ya bada umarnin rufe dukkan asusun gwamnati bayan ya karɓi mulki, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan kuɗi ya kara da bayanin cewa gwamnatin Ortom ta nuna wa Gwamna Alia asusu 25 ne kacal lokacin da ya karɓi ragamar mulki a watan Mayu.

Amma a cewarsa, bayanai daga hukumar kula da mu'amalar bankuna ta tarayya ya nuna gwamnarin Benuwai na da asusu sama da 600.

"Lokacin da muka zo, mun nemi a bamu bayanan asusun banki kuma an gabatar mana da asusu 25. Da muka duba tsarin kula da mu'amalolin banki ya nuna jihar Nenuwai tana da asusu sama da 600."
"Saboda haka ne gwamna ya ga ya kamata a rufe dukkan waÉ—an nan asusu domin gano me ke faruwa."

Oglegba ya jaddada cewa gwamnatin Alia ta gaji bashin N359bn wanda ya ƙunshi basukan da ake bin ƙananan hukumomin jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN