Abun mamaki yayin da Lauyan bogi ya yi nassara a sharioi 26 a gaban manyan alkalai kafin a kama shi



Hukumomin kasar Kenya sun kama wani lauya na bogi, Brian Mwenda, wanda ya yi nasara a kararraki 26 a lokacin da yake gabatar da kansa a matsayin lauyan babbar kotun kasar Kenya.

 Rahotanni sun ce lauyan ya gudanar da kararraki 26 a gaban alkalan manyan kotuna da alkalan kotun daukaka kara infa ya yi nassara a shari'ar da ya wakilta kafin a kama shi.

 Kungiyar Lauyoyi ta Kenya (LSK) reshen Nairobi Rapid Action Team (RAT) ta kama shi saboda sha'anin karya, lokacin da suka sami korafin jama'a.


 Reshen Nairobi ya bayyana a shafinsu na X cewa shi ba lauya ba ne kuma ba shi da lasisin yin aikin lauya a Kenya.

 "An gabatar da shi ga LSK Branch Nairobi ta hanyar Ƙungiyar Rapid Action Team (RAT), cewa mutumin ya kasance yana gabatar da kansa a matsayin Lauyan Babban Kotun Kenya kuma memba na LSK Nairobi Branch,"

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN