Jerin kaya fiye da 40 da ya halasta a shigo da su Najeriya tun bayan haramta su a 2015, har da shinkafa, siminti, saura..


Babban bankin CBN ya cire takunkumin da ya kakaba wajen shigo da wasu kayayyaki tun shekarar 2015.

Sanarwar da babban bankin ya fitar ta bakin Dr. Isa Abdulmumin a shafukansa a ranar Alhamis ya yi bayanin matakin da aka dauka. Legit.ng ya wallafa.

Rahoton ya tattaro jerin duka sunayen kayayyaki da yanzu ya halatta ‘dan kasuwa ya samu kudi domin ya shigo da su.

Kafin yanzu, The Cable ta ce masu bukatar sayo wadannan kaya daga kasashen ketare, su na neman kudi ne da tsada a kasuwar canji.

CBN ya yi hakan ne domin yunkurin tallafawa kamfanonin gida da su ke samar da wadannan kaya da kuma tsare mutuncin Naira.

Ga jerin kayan nan kamar haka:

Kayan da CBN ya cirewa takunkumi
1. Shinkafa

2. Siminti

3. Bota

4. Kayan man gyada, man ja da sauransu

5. Nama da kayan nama

6. Ganye da sauran kayan ganye

7. Kaji, kwai, zabi

8. Jiragen sama/jiragen yawo

9. Turaren wutan Indiya

10. Kifin gwangwani

11. Nadadden rodi

12. Shafaffen rodi

13. Kwanon gini

14. Baro

15. Kwanon daukar kaya

16. Akwatin karfe da garwa

17. Kayan tangaran

18. Gangunan karfe

19. Bututun rodi

20. Wayoyin rodi

21. Rodi

22. Karfen waya

23. Kusoshi

24. Wayar tsaro

25. Allon katako

26. Faifen allo

27. Filai wood

28. Kofofin katako

29. Kayan jeren gida

30. Tsinken sakace

31. Gilas

32. Kayan girki

33. Kayan tebura

34. Tayil

35. Tufafi

36. Kayan auduga

37. Yadi/shaddoji/leshi da saurasu

38. Robobi da kayan roba

39. Sabulu da kayan kwalliya

40. Tumatur da tumaturin leda (ko gwangwani)

41. Sayen kudin kasar waje/hannun shari/da sauransu

42. Masara

43. Takin zamani

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN