“Na yi dana sanin tallata Buhari”, Rarara ya fadi gaskiyar abin da ya faru


Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahuru Rarara ya caccaki Buhari kan irin yadda ya gudanar da mulki a kasar. Legit Hausa ya wallafa
.

Rarara ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da hadiminsa, Rabi’u Garba Gaya ya yada a kafar sadarwa.

Kahutu ya ce Buhari sai da ya kashe kasar nan sannan ya sake ta bayan ya lalata komai a kasar.

Ya ce ya kamata mutane su fito su fadi gaskiya amma sun gagara inda ya ce a lokacin PDP an bayyana cewa kasar a mace ta ke don haka mutane su ka amince da Buhari.

A cewarsa:

“Sun kasa fitowa su fada wa mutane gaskiya, Buhari sai da ya kashe kasar nan sannan ya sake ta, Buhari ya yi dama-dama da kasar nan, su fito su fadi gaskiya ba wani abu ba ne.

“Lokacin da mu ka karbi mulki a hannun PDP, an fada an ce kasar nan a mace ta ke, abin da ya sa mutane su ka yi wa Buhari uzuri kenan, me yasa mu yanzu za mu boye.”

Mawakin ya ce ya yi dana sanin tallata Buhari ta wani bangare sannan a wani bangare bai yi ba, saboda kyakkyawan zaton da ya yi wa Buhari.

Ya ce da ya san abin da ke kasa da bai yi wannan talle na Buhari ba, sai dai ya ce bai yi dana sani ba saboda ya yi ne don Allah.

Ya kara da cewa tabbas ya yi makauniyar soyayya amma mutane sun san gaskiya kuma sun yi shiru bayan ya yi dama-dama da kasar.

A wani labarin, mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya gamu da tsautsayin hatsarin mota.

Sai dai an tabbatar cewa mawakin bai samu ko kwarzane ba, lamarin ya faru ne yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukan jiragen sama.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN