Yan Najeriya sun mayar da martani bayan da dan shugaban kasa Seyi Bola Tinubu, bayan ya shigo jirgin shugaban kasa domin kallon gasar kwallon Polo a Kano ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa dan shugaban kasar ya je Kano ne domin kallon gasar Polo ta kasa da kasa ta NPA ta Kano ta shekarar 2023 a filin wasa na Usman Dantata Polo. Daily trust ta rahoto.
‘Yan Najeriya sun yi ta yada bacin ransu kan lamarin, yayin da wasu da dama ke cewa iyalan Tinubu sun mayar da arzikin kasar nasu.
Wasu ’yan Najeriya sun ce iyalan shugaban ba su damu da halin kuncin da talakawa ke ciki ba a yayin da ake cire tallafin man fetur ba tare da ingantattun hanyoyin magance illar da yin hakan zai haifar ba.
A cikin hotunan da aka dauka a shafukan sada zumunta, Seyi yana tare da jami'an tsaro, lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Kano, inda wakilin Kwankwasiyya ya tarbe shi, wata kungiya mallakin Rabi'u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar (New Nigeria Peoples Party). NNPP).
DAGA ISYAKU.COM