Kotu ta yanke wa ASP na yan sandan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar rataya, duba dalili


Mai shari’a Ibironke Harrison na wata babbar kotun jihar Legas ta yanke wa dan sanda ASP Drambi Vandi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe lauya, Barista Bolanle Raheem.

 Vandi ya harbe Misis Raheem har lahira a gaban mijinta yayin da take dawowa daga coci a ranar Kirsimeti 25 ga Disamba, 2022 a wani shingen bincike na 'yan sanda a Legas.

 Da take yanke hukunci a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, kotun ta samu mataimakin Sufeton ‘yan sandan da aka dakatar da laifin kashe lauyan ranar Kirsimeti ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 An gurfanar da Mista Vandi a gaban kotu a ranar 16 ga watan Janairun 2023, kan zargin kisan kai amma ya ki amsa laifinsa.  Kotun ta ba da damar ci gaba da sauraron karar.

 Gwamnatin jihar Legas ta ce Vandi ya harbe Misis Raheem a kirji a ranar 25 ga Disamba, 2022, a Ajah Roundabout, kan titin Lekki- Expressway, jihar Legas.  Gwamnatin jihar ta shaidawa kotun cewa laifin ya sabawa sashe na 223 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN