Yaro dan shekara 19 ya yi wa kaninsa duka har ya binne shi da rai bisa zargin satar Naira 1000 a jihar Kogi


Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kama wani matashi mai suna Goodness Oshodi mai shekaru 19 da haihuwa da ake zargin ya binne kanensa mai suna Friday Oshhodi da ransa bisa zargin satar Naira 1000.

 Lamarin ya faru ne da yammacin Talata 10 ga watan Oktoba, 2023, a unguwar Apamisede, a karamar hukumar Adavi ta jihar.

 Sai dai wanda abin ya shafa ya yi sa'a da makwabta sun ceto shi.

 A cewar shaidun gani da ido, mahaifiyar Goodness ta umarce shi da ya hukunta Friday bisa zargin satar mata N1000.

 An tattaro cewa Goodness ya lakada wa Friday duka kafin ya binne shi da rai.

 Da yake magana kan dalilin da yasa ya yanke shawarar binne dan uwansa da rai, Goodness ya ce yana aiwatar da umarnin mahaifiyarsu ne kawai da ta bukaci ya hukunta dan uwansa bisa zargin satar mata N1000 da kokarin gudu.

 A cewarsa, mahaifiyar wadda ta umarce shi da ya hukunta Friday, ta je coci lokacin da ya binne shi da rai.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP William Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama yaron kuma ana yi masa tambayoyi.

 “Eh, muna sane.  An kama yaron, ana ci gaba da gudanar da bincike kan dalilin da ya sa kuma ta yaya hakan zai iya faruwa,” PPRO ya kara da cewa.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN