Sama da 'yan Isra’ila 600 ne ake fargabar sun mutu yanzu haka kuma wasu dubbai sun jikkata sakamakon harin da ba a taba ganin irinsa ba daga mayakan Hamas suka kai Isra'ila.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce akalla mutane 600 ne suka mutu yayin da wasu 2,000 suka jikkata a harin na ranar Asabar.
Mayakan Hamas sun kuma yi garkuwa da fararen hula da sojoji da ba a san adadinsu ba zuwa Gaza.
Dakarun tsaron Isra'ila sun fitar da faifan harin makami mai linzami da ta yi ikirarin kai hari kan wani fili mallakin shugaban hukumar leken asirin soji ta Hamas, inda ta kara da cewa ta kai hari kan wasu bankuna biyu na kungiyar ta'addanci da kuma wuraren kera makamai ta sama a Gaza.
"Ya zuwa wannan sa'a, akwai dakarun sojin Isra'ila da ke fafatawa a [Kibbutz] Kfar Aza, ana bincike a garuruwa da dama. Akwai dakarun IDF a dukkan garuruwa, babu wani garin da ba shi da rundunar IDF a cikinsa, "in ji shi a cikin jaridar The Times of Israel.
Da yake magana a wani taron tattaunawa da safiyar yau, ya kara da cewa: "Harin Hamas" munanan harin laifi ne na yaki.
DAGA ISYAKU.COM