Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a ranar Lahadi ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana neman izinin gwamnatin tarayya domin jami’anta su fara rike makamai a wajen aiki.
A wata sanarwa da jami’in ilimin jama’a nanFRSC na kasa, Assistant Corps Marshal Bisi Kazeem ya fitar a Abuja, ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton.
“An jawo hankalin hukumar FRSC kan wani rahoto da ke nuna cewa jami’an hukumar na neman izinin gwamnatin tarayya domin jami’an hukumar su dinga daukan makamai zuwa wajen aiki.
“Maganganun kuskuren da wakilin corps Marshal ya yi a wajen bikin faretin na FRSC a garin Kotangora na jihar Niger, bai yi daidai da matsayin shugaban hukumar da jami’an gudanarwar a halin yanzu ba,” in ji Kazeem.
DAGA ISYAKU.COM