Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kama wani matashi mai suna Olamilekan Afeez mai shekaru 30 da haihuwa, bisa laifin cin zarafin wani dan sanda da ke aiki a sashen rundunar yan sanda na Okeigbo.
Wani faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo ya nuna mutumin yana marin dan sandan da ke bakin aiki a mahadar Ago Jedi T.
Har yanzu dai ba a san musabbabin takun saka tsakanin mutumin da jami'in ba.
DAGA ISYAKU.COM