Wani mai wankin mota ya sallake rijiya da baya lokacin da ya yi hatsari da matar lokacin da ya gwada tukata a unguwar Rumueme da ke Fatakwal a Jihar Ribas.
Mai amfani da Facebook, Justice Ori wanda ya wallafa hotuna daga wurin ya ce lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, 29 ga Oktoba, 2023.
“Ya faru da yammacin yau a unguwar Rumueme da ke Fatakwal. Wani mutum ya tuka motarsa ya nufi wajen wankin mota, mai wankin mota bayan ya wanke motar ya yanke shawarar gwada kwarewarsa ta hanyar tuka motar, abu na gaba da muka gani shine motar ta tsundumq a cikin magudanar ruwa.