Zanga zanga ta barke a Kano sakamakon shirin Gwamnati na rushe wani aikin da APC ta yi


Mazauna garin Gwarzo a Arewacin jihar Kano su na Allah wadai da abin da su ka kira yunkurin rushe wata gada da ‘dan majalisar APC ya gina. Legit ya wallafa.

Premium Times ta ce kwanakin baya ruwa ya share wata gada da ke Gwarzo, nan take al’ummar yankin su ka nemi taimakon Sanatansu, Barau Jibrin.

Kafin a ce kobo, Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa kuma mataimakin shugaban majalisa ya yi sanadiyyar da aka gyara muhimmiyar gadar.


A ranar Juma’a aka kammala aikin gadar, Jibrin shi kadai ne Sanatan APC a majalisa daga Kano, watakila abin da ya faru bai yi wa NNPP mai mulki dadi ba.

Wani direba mai suna Sule Wanzom, ya shaidawa jaridar cewa a ranar Juma’ar nan mazauna garin Gwarzo su ka fara zanga-zanga da jin take-taken gwamnati.

Ana kishin-kishin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na so ta ruguza gadar domin ta gina wanda ya fi shi kyau, har ranar Asabar zanga-zangar ba ta tsaya ba.

Wanzam ya ce gadar ta na da matukar muhimmanci a yankin kuma ta na kai wa har kauyen mataimakin gwamna mai-ci, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Gadar ta jona da gidan Aminu Abdussalam Gwarzo wanda hakan ya jawo ‘yan jam’iyyarsa (New Nigeria People Party) a kauyen su ka ji babu dadi.

Mazauna su na da ra’ayin cewa sabanin siyasa ya jawo ake so a ruguza wannan aiki ba komai ba, ‘Yan jam’iyyar APC sun nuna ba za su amince a rusa ba.


Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN