Dalibin mataki na 100 ya yanke jiki ya fadi ya mutu a makarantar horar da hafsoshin yan sanda a Kano


Wani dalibi dan sanda mai matakin kwas 100, Suleiman Jika, ya rasu bayan da ya fadi a makarantar horas da ‘yan sanda ta Najeriya da ke Wudil a jihar Kano. 


 Jika, mai shekaru 19, wanda ya fito daga Jihar Adamawa, kuma yana Sashen Kimiyyar Na'ura mai Kwamfuta, an ruwaito cewa ya yanke jiki ya fadi ne a cikin bandaki da sanyin safiyar Asabar, 2 ga watan Satumba, 2023.


 Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wasu daga cikin daliban kwalejin sun zargi kwamandan, mataimakin sufeto-janar, Sadiq Abubakar, da “tsanantawa da kuma almundahana da kudaden alawus-alawus na ciyar da daliban.


 Wani dalibi, wanda ya yi magana da jarida bisa sharadin sakaya sunansa don gudun kada a ci zarafinsa, ya ce an garzaya da dalibin zuwa asibitin makarantar.


 Majiyar ta kara da cewa "Ba a kula da shi ba saboda babu wani magani da kuma wani jami'in lafiya da zai kula da shi a cikin yanayi mara kyau, kafin daga bisani ya mutu."


 Wani dalibi wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a kullum ana samun cunkoson dalibai marasa lafiya a asibitin da baya  da kayan aiki mai kyau.


 "Tun da sabon kwamandan ya hau karagar shugabancin kwalejin, suna ba mu abinci mara kyau da rashin isassun abinci.  Yaron da ya rasu bai kai shekara 20 ba.  Yaron ba zai mutu ba idan ya sami kulawar gaggawa kuma ingantacce.  Kwamandan ya kuma ba da umarnin rufe kasuwar makarantar da wajen wanki da kuma amincewa da atisayen da ba su dace ba a lokacin lacca,” in ji dalibin.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN