Dubu dubatan Yan kasar Nijar sun mamaye barikin sojin kasar Faransa da ke Niamey suna neman sojin su fice daga kasarsu.
Rahotun Aljazeera ya ce akwai sojin Faransa 1500 a kasar Nijar wanda yan Nijar a halin yanzu ke neman su fice daga kasar su.
Rahotanni sun ce jami'an tsaron Nijar suna ta lallashin dubban matasan, wadanda suka ce ba za su bar wajen ba sai sojin Faransa sun fice daga kasarsu.
Published by isyaku.com