Yawa ta balle: An yi wa sojojin bogi guda 5 kamun kazan kuku a Najeriya


 Rundunar sojojin Najeriya Brigade ta 9, da ke Ikeja Cantonment a jihar Legas, ta kama wasu mutane biyar da ke yin sojin bogi. 

 Wadanda ake zargin da aka mika wa ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban Kotu, an ce an kama su a lokuta daban-daban a yankunan Ojodu Berger, Ikorodu, Ogba, da Ikeja a Legas.

 Wadanda ake zargin dai sun hada da Johnson Ayemoba, Salami Olamilekan, Mumammed Bilyaminu, Abijo Taofeek, da Adewale Quadri, a cewar daraktan hulda da jama’a na rundunar ta 9, Manjo Augustine Kolawole, an kama su ne a wani sintiri na yau da kullun da rundunar ta Brigade ta yi.

 Tuni rundunar yan sandan jihar Lagos ta fara bincike domin gurfanar da sojojin bogi da soji suka kama suka mika mata.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN