Da dumi: Jarirai 2, a mutane 34 sun kone kurmus sakamakon tashin gobara a barauniyar ma'ajiyar man fetur a..


 Fashewar barauniyar ma'ajiyar man fetur  a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 34.

 Wani jami’in gwamnati ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin ranar Asabar. Vanguard ta rahoto.

 Jami’in gwamnatin kasar ya ce akalla mutane 34 ne suka mutu a lokacin da wata jijiya ta haramtacciyar man fetur ta kone kurmus a kudancin Benin da ke kusa da kan iyaka da Najeriya.

 Ministan harkokin cikin gida Alassane Seidou ya shaidawa manema labarai cewa: "Mummunar gobara ta tashi a garin Seme Podji."

 “Abin takaici mun sami mutuwar mutane 34 ciki har da jarirai biyu. Gawarwakinsu sun kone saboda musabbabin tashin gobarar man fetur ta barauniyar hanya.”

 Ministan ya ce wasu mutane 20 na jinya a asibiti, ciki har da wasu da ke cikin mawuyacin hali.

 Najeriya dai kasa ce mai arzikin man fetur da iskar gas kuma ana yawan safarar man fetur a iyakokinta, musamman ma lokacin da gwamnati ta ci gaba da bayar da tallafin rage farashin man fetur.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN