Yanzu yanzu: Yan sandan jihar Kebbi sun kama dubu-dubatan kullin tabar wiwi da ba a taba kama irinsa ba a tarihin jihar Kebbi


Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta kama manyan motoci guda biyu makare da kullin tabar wiwi da ba a taba kama irinsa ba a tarihin tsaro a jihar Kebbi.

A motar ta farko mai lamba IT 21520 LA, Lagos, yan sanda sun kama surkin kullin wiwi guda 4,927 da aka kiyasta kudinsa ya kai fiye da N300m. 

Yan sanda sun kama mutane uku masu suna Emmanuel Chukwuma dan asalin karamar hukumar Banden a jihar Abia, da Kanta Bisa dan karamar hukumar Asaka a kasar Ghana, tare da Ishola Adeyemi, dan Unguwar Alufon, a karamar hukumar Akure na jihar Ondo dangane da kayakin.

Kazalika Yan sanda sun sake kama wata motar mai lamba IT 21608 LA, Lagos, makare da surkin kullin tabar wiwi guda 4,906. Yan sanda sun kama wani mai suna Abdulrazak Agboola, dan asalin Unguwar Yana Ajiya a birnin Ibadan, dauke da kayakin a cikin babbar motar.

An kiyasta cewa, jimillar kiyasin kudin surkin tabar wiwi da Yan sanda suka kama ya zarce N600m.

Binciken Yan sanda ya nuna cewa an yi hayan direbobin motocin ne daga kasar Ghana domin su kawo tabar wiwi a kan kudi N200,000 a mota tafako yayin da aka yi alkawarin biyan N400,000 ga direban mota na biyu.

Yan sanda sun kuma kama albarushi Cartridges katon 30 wanda ke dauke da kwali goma a kowanne kuma akwai kwara 25 a ciki.


Kakakin rundunar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya ce, sashen binciken manyan laifuka na rundunar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. 

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN