Illustrative picture Photo credit: Accord Newspaper |
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke wata mata bisa mutuwar mijinta, Jakpo Ekemini, a unguwar Mosogar da ke karamar hukumar Ethiope ta Yamma a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Warri a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, 2023, ya ce matar ta ja mazakutar mijin nata mai shekaru 32 a duniya a lokacin wata rigima a tsakaninsu.
“Ba ta yanke mazakutar ba, sai dai ta damke su day karfi ta ja su,” in ji PPRO.
"Mutumin ya mutu sakamakon wannan lamari," in ji shi.
Wata majiya da ta san lamarin, ta shaida wa manema labarai cewa, babban yayan marigayin ne ya kai rahoton lamarin a ranar Talata ga ‘yan sandan yankin da ke Mosogar.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata 12 ga watan Satumba da misalin karfe 1:20 na rana sakamakon rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin ma’auratan.
“Matar kanena (an sakaya sunanta) ta damke kuma ta ja mazakutar mijinta, Efemini, mai shekara 32 a lokacin da suke fada a Mosogar. Ana cikin haka sai kanina ya fadi aka garzaya da shi asibiti inda daga baya aka tabbatar da cewa ya rasu. An ajiye gawar a dakin ajiyar gawarwaki da ke Mosogar,” majiyar ta ruwaito dan uwan marigayin yana cewa.
An tattaro cewa wanda ake zargin ta gudu zuwa inda ba a sani ba bayan ta aikata laifin. Daga baya an kama ta kuma a halin yanzu ana yi mata tambayoyi a hannun yan sanda.
Published by isyaku.com