Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers a ranar Laraba, ta fitar da sanarwar a hukumance tana neman Gift David Okpara, wanda aka fi sani da 2 Baba, shugaban kungiyar asiri. PM News ta ruwaito.
2 Baba sanannen shugaban kungiyar asiri ne a Iceland, wanda ya kashe jami’in ‘yan sanda shiyya DPO na Ahoada reshen jihar Ribas, SP Bako Angbashim.
Ofishin Sufeto Janar na ‘yan sanda, sashen binciken manyan laifuka na rundunar, FCID, rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, ta yi alkawarin bayar da tukuici ga duk wanda ya bayar da bayani da zai kai ga kama shugaban kungiyar ‘yan daba da ake nema ruwa a jallo.
Laifukan da aka lissafa a kan sa sun hada da: hada baki, kasancewa Dan kungiyar asiri da kuma kisan SP Bako Angbashim, jami'in 'yan sanda na Dibisional (DPO) na Ahoada reshen jihar Ribas.
Rundunar ta shawarci jama’a da su kira 08098880134, 08032003514,08098888801, 08037921407 da 08161355218 domin kai rahoton duk wani bayani da zai kai ga kama shi.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya kuma bayar da kyautar Naira miliyan 100 domin a ba duk wanda ya bayar da sahihan bayanan da za su kai ga kama shi.
Published by isyaku.com