Yamutsi ya kaure yayin da manbobin NURTW suka yi wa juna duka a Abuja


An shiga tashin hankali da firgici a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, lokacin da tsagin ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa (NURTW) suka ba hammata iska. Legit Hausa ya wallafa.

Shaidar ganau ba jiyau ya tabbatar da cewa an yi harbe-harben bindiga a lokacin rikicin, cewar rahoton Channels tv.

Da yake magana bayan ya nemi a sakaya sunansa, shaidar gani da idon ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da cewa bindigun da aka harba daga ɓangaren ƴan sanda ne ba, ko mambobin ƙungiyar masu faɗa da juna

An tattaro cewa rikicin ya auku ne a tsakanin mambobin ƙungiyar da ke biyayya ga shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tajudeen Baruwa, da magiya bayan abokin hamayyarsa Badru Agbede, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Baruwa ya sha yin kira ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da ta sanya baki domin a warware rikicin, ta yadda za a dawo da mambobinsa a hedikwatar ƙungiyar ta ƙasa wacce a yanzu haka take a ƙarƙashin ikon ƴan sanda.

Jami'an ƴan sanda har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba su ce komai ba dangane da rikicin da ya auku.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN