Bayan sace wayoyin lantarkin transfomar Bayan Kara a B-kebbi, Kotu ta yi wa mutanen daurin shekaru...


Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Birnin kebbi ta yanke wa wasu mutane biyu da suka gurfana a gabanta hukunci bayan samunsu da laifin satar wayoyin na’urar taransfoma a shiyar Nahuta da ke unguwar Bayan Kara a Birnin kebbi.


 Alkalin kotun Majistare Samaila Kakale Mungadi, ya yanke hukuncin daurin shekara daya kowanensu ga Nuhu Ahmed da Yazidu Ahmed,  kowannensu kan laifin hada baki, daurin shekaru biyu kowannensu saboda laifin sata, ba tare da zabin biyan tara ba bayan an same su da laifi kamar yadda aka tuhumesu karkashin sashe na 60, 272 na kundin laifuffuka na jihar Kebbi. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com  tun da farko ya ruwaito cewa mutanen sun amsa laifinsu a kotu da ya gabata.


 Mutanen biyu da aka yankewa hukuncin za su kuma biya diyyar N971,000, wanda ya karbi kayan da aka sace ya biya N350,000.  Wadanda aka yanke wa hukuncin za su biya ragowar kudin ko kuma su yi zaman Kurkuku na shekaru biyu kowannensu.


 Kenan wadanda aka yanke wa hukuncin za su yi shekara biyar a cikin gidan gyara hali idan sun kasa biyan diyya.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN