An kwantar da wata ‘yar Amurka a asibiti bayan da wani mutum ya ci zarafinta saboda ta ki ba shi lambarta.
Lamarin ya faru ne a jihar Texas ta Amurka. A daya daga cikin faifan bidiyon da ta watsa a shafinta na Instagram, matar ta bayyana cewa maharin ya buge ta da bulo a fuska yayin da sauran mazan da ke wurin ba su yi wani abin da zai hana shi ba.
A wani faifan bidiyo daga gadon asibitinta, matar da ke cikin hawaye, ta ce tana tsoron ba za a kama maharin nata ba bayan ya shiga motarsa ya bar wurin.
Published by isyaku.com