Mutane 3 sun mutu a Kebbi sakamakon tsanani da ambaliyar ruwan sama


Ambaliyar ruwa da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ta dauki tsawon sa'o'i da dama ta yi sanadiyar mutuwar mutane uku a yankin Dakingari da ke karamar hukumar Suru a jihar Kebbi. LIB ya ruwaito.


 Shugaban karamar hukumar Suru, Alhaji Muhammad Lawal Suru ya ce ambaliyar ta dauki tsawon sa’o’i da dama tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.


 Suru ya ce;


 “Bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan da ke gangarowa daga tsaunukan da ke kewayen garin Dakingari ya taimaka wajen ambaliya.


 “Sama da shekaru ashirin muna fama da ambaliyar ruwa idan ana ruwan sama duk shekara.  Gwamnatocin Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu da suka shude sun gina magudanan ruwa a garin domin magance matsalar amma ba su hana ambaliyar ruwa ba duk shekara”.


 Shugaban karamar hukumar wanda ya yi kira ga al’ummar yankin da su daina kafa gine-gine da zubar da shara a kan magudanan ruwa, ya kuma ce za a iya hana ambaliyar ruwa idan za a iya gina katanga da mashigar ruwa a kewayen tsaunukan.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN