Yan sandan Kebbi sun karyata jita-jitan bayyanar masu sallama a gida daga nan sai a fita hayyaci a Birnin kebbi


Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta karyata jita-jita da ke yawatawa cikin garin Birnin kebbi cewa wasu mutane sun bayyana masu Karfin saddabaru da rauhanai.

Rundunar ta ce binciken da Yan sanda suka yi kan lamarin ya nuna cewa wannan jita-jita ba gaskiya bane.

Wannan na kunshe a wata takardar sanarwa da ta fito daga ofishin kwamishinan Yan sanda ta hannun Kakakin rundunar na jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ranar Litinin 4 ga watan Satumba wanda shafin labarai na isyaku.com ya samu..

Sanarwar ta ce:

"Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta karyata wani jita-jita da ake yadawa na cewa akwai jama’a masu saddabaru da suka bayyana a yankin Malala da Bayan Gidan Sarki a cikin  Birnin Kebbi.

 Jita-jitar ta yi zargin cewa akwai mutanen da ke da ikon rauhanai a cikin Birnin Kebbi, ayyukan da ke barazana ga tsaro da lafiyar jama'a.  Sai dai bincike na farko ya nuna cewa, jita-jita da ake yadawa wanda ke haifar da fargaba, an gano ba gaskiya ba ne.

 Rundunar ta na amfani da wannan kafar wajen yin kira ga al’ummar jihar Kebbi masu son zaman lafiya da su yi watsi da irin wannan jita-jita, domin ba ta da inganci da kwararan hujjoji.

 Dangane da wannan batu, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, CP Samuel Titus Musa, psc yana kira ga al’ummar jihar Kebbi da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da fargabar irin wannan jita-jita ba, kamar yadda rundunar ta bayyana cewa ta fara aiki, Kuma tana shirye don fuskantar duk wani yanayi da ba a zata ba.

 A karshe, ana gargadin jama’a da su daina tada hankalin jama'a ta hanyar yada karya a kan wasu mutane, tare da daukar doka a hannunsu maimakon kai rahoto ga hukumomin da suka dace don daukar matakin da ya dace.

Saboda haka, duk wanda aka samu yana da laifi, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya, don Allah a kiyaye".

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN