Yadda ta faru a kasuwannin Kano bayan hukuncin Kotu tsakanin Abba da Gawuna


An rufe kasuwanni da dama a Kano biyo bayan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ta yanke.

 Akwai kuma rahotannin murna daga magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress. PM News ta rahoto.

 Kotun da ke da wasu mambobi irin su Justice Flora Azinge ta kori Gwamna Abba Yusuf na Jam’iyyar NNPP tare da bayyana Nasir Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

 An yanke hukuncin ta hanyar Zoom, bayan barazanar da aka yi wa mambobin kotun.

 Alkalan dai ba su halarci kotun ba a lokacin da aka yanke hukuncin.

 Bayan yanke hukuncin, ‘yan kasuwar sun rufe shagunansu suka bar kasuwanni irin su Sabon Gari, Kantin Kwari da kuma Singer.

 An kuma rufe babban kantin sayar da kayayyaki a cikin birni, da Ado Bayero Mall (ShopRite).

 Kotun ta amince da daawar lauyoyin APC cewa, kuri’u 165,663 da aka kirga wa Abba Yusuf a zaben ba a sanya hannu ba, ko kwanan wata.

 Ta haka ta cire kuri’un daga adadin jimillar kuriun zabe Wanda ya tayar da nasarar Abba zuwa Gawuna.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN