Cikin Mataimakin Gwamna ya duri ruwa bayan Yan Majalisar dokokin jiharsa 23 cikin 26 sun sa hannu kan zancen tsige shi


A ranar Laraba ne ‘yan majalisar dokoki a jijar Ondo suka fara shirin tsige mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa.

 Hakan dai na faruwa ne duk da musantawa da ‘yan majalisar suka yi cewa babu wani shiri na tsige Aiyedatiwa. Jaridar The Nation ta rahoto.

 Aiyedatiwa a makon da ya gabata ya ce ba zai yi murabus daga gwamnatin Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ba.

 Ya kuma bukaci ‘yan majalisar da su yi watsi da duk wata wasika da ake yadawa da ke nuni da cewa ya yi murabus.

 Mataimakin Gwamnan ya ce ya yi rantsuwar kare kundin tsarin mulkin kasa, kuma yana da wa'adin shekaru hudu a karagar kujerarsa.

 To sai dai kuma, a wani yanayi na daban, Majalisar ta kira zaman taron gaggawa a ranar Laraba.

An jibge jami'an tsao a titin da ta bi zuwa harabar majalisar.

 Jami'ai na binciken duk motocin da ke shiga ta hanyar harabar Majalisar.

 An tattaro cewa ‘yan Majalisa 23 daga cikin 26 sun sanya hannu kan takardar tsige mataimakin gwamnan.

Published by isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN