Babban Darakta na asibitin kwararru na jihar Ekiti, Ikere-Ekiti, Dakta Olubiyi Olaolu Abidemi ya yi wa matarsa dukan tsiya sakamakon rashin jituwa da suka samu a gidansu da ke asibitin St. David Compound Ifaki-Ekiti a ranar Alhamis, 14 ga Satumba, 2023.
Vanguard ta ruwaito cewa Likitan ya fusata ne bayan da matarsa ta ki kula da wata abokiuarsa (ma’aikaciyarsa) kamar yadda ya umarce ta.Wani dan uwan matar ya shaida wa jaridar cewa Likitan ya yi barazanar kashe ta kuma ya kama wuyanta ya yi yunkurin shake ta a gidansu.
Matarsa mai suna Dokta (Mrs) Olubiyi Adenike, malama a Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti, an bayyana cewa ta samu munanan raunuka a wuyanta kuma an kwantar da ita a sashin hadurran da gaggawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti.
An kuma tattaro cewa CMD wanda ya ki yin magana da manema labarai lokacin da aka tuntube shi, ya yi ikirarin cewa matarsa tana riya duk da an kai ta asibiti.