Duk ta tsige shi da Kotu ta yi, Gwamna Yusuf ya kara yawan mataimaka na musamman zuwa 144

 

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya kara adadin mataimakansa na musamman zuwa 144 tare da nada karin guda 94.

 Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Malam Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Kano ranar Talata. NAN ta rahoto.

 A baya gwamnan ya nada mataimaka na musamman guda 57, wanda ya kawo adadin zuwa 144

 Mata biyar ne kawai daga cikin sabbin mataimaka 94 da gwamnan ya bayyana.

 Sun hada da Rahama Kabeer Fagge, babban mai bayar da rahoto na musamman na gidan gwamnati;  Amina Isah Bebeji, Wakiliya ta musamman, SEMA;  Maijidda Garba, Wakili na Musamman, REB;  Fatima Usman Muhammad, babbar mai bayar da rahoto ta KNARDA;  da Asiya Muhammad Umar, mai ba da rahoto ta musamman, Cibiyar Kula da BaĆ™i.

 Dawakin -Tofa ya ce dukkan nade-naden sun fara aiki nan take.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN