Uwargida ta kwada wa maigida tabarya a kai har sau 3 ta aika shi lahira yayin da yake barci da rana tsaka, duba dalili


Wata mahaifiyar ‘ya’ya uku, Misis Tayelolu Solomon, ta kashe mijinta mai shekaru 65 mai suna Felix Solomon bayan ta kwade shi da tabarya a kai  a jihar Ondo.

 A cewar jaridar mallakar gwamnatin jihar, lamarin ya faru ne a GRA da ke garin Ondo a karshen mako.

 An tattaro cewa ma’auratan sun sha fama da rikicin cikin gida, kuma matar ta yi barazanar kashe shi.

 A cewar dan marigayin, Ibukun SolomonIbukun Solomon wanda lamarin ya faru a gaban idonsa, mahaifiyarsa ta kashe mahaifinsa yayin da yake barci bayan wata ‘yar gardama.

 “Mahaifiyata ta kashe mahaifina da tabarya a gabana, kuma sai ta gudu.  Ta yi amfani da tabarya ta buga masa a kai lokacin da yake barci,” inji shi.

 “Tun da farko dai wata ‘yar karamar gardama ta shiga tsakaninsu wanda hakan ya haifar da fada, bayan fadan ne mahaifina ya je ya kwanta akan kujera sai mahaifiyata ta buga masa tabarya a kai.

 “A cikin haka sai ya sume ya fado daga inda yake barci, mahaifiyata ta yi amfani da tabaryar ta buga wa mahaifina a kai har sau uku, daga baya ya mutu.

 “Lokacin da mahaifiyata ta ga mahaifina ya riga ya sume, sai ta boye makamin a bayan gidanmu, ta gudu.

 "Na sanar da wasu mazauna garin, inda suka garzaya da mahaifina asibiti, amma daga baya ya mutu. An ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa. Mahaifiyata ta haifi 'ya'ya uku ga mahaifina kuma ni ne yaro na karshe."

 An tattaro cewa gawar marigayin yana cikin gidan har jama’ar unguwar suka isa wurin.  Kuma sun kira 'yan sanda don neman taimako.  An kuma tattaro cewa marigayin ya shirya kai rahoton matar ga iyalanta kafin ta tura shi kabarinsa.

 Wani daga cikin iyalan mamacin ya ce suna kokarin sasanta rikicin da ya barke tsakanin ma'auratan kafin wannan bala'i ya afku.

 Majiyar ta bayyana cewa ba shi ne karon farko da irin wannan takun saka tsakanin ma’auratan ya faru ba.

 “Matar ta kasance tana yi wa mijinta barazanar cewa za ta kashe mijinta a duk lokacin da suke fada, kuma marigayin ya sanar da mu wannan barazanar, amma ba mu taba sanin za ta aiwatar da hakan ba, amma a wannan karon ta dauki doka a hannunta, ta kashe dan uwanmu.  ba don komai ba, dole ne a kama ta a gurfanar da ita a gaban kuliya.”

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN