An gudanar da addu'a ta musamman ga Gwamnan Kebbi a babar Masallacin Idi na garin Birnin kebbi

 

A ranar Laraba ne kungiyar Kauran Gwandu Achievement Forum ta shirya addu’a ta musamman ga sabuwar gwamnati a jihar Kebbi karkashin jagorancin Kwamared Dr Nasir Idris domin cimma manufofinta  na kawo sauyi a jihar.

 Addu'ar wadda aka shirya karkashin jagorancin shugaban kungiyar Alhaji Shu’aibu Garba Tazarce ta gabatar da taron addu’o’i da Malamai daban-daban suka gudanar a filin Sallar Idi na Birnin Kebbi.

 Malamai sun hada da;  Malam Imrana Usman, Babban Limamin Masallacin Juma'a, Bayan Oando, Birnin Kebbi, Sheik Muhammad Tukur Argungu, Babban Masallacin Juma'a na Argungu, da sauran Limaman Masallatan Juma'a.

 Malamai sun roki Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa Gwamna Nasir Idris baiwa da hikimar tafiyar da al’amuran jihar da kyau.

 A yayin da suke addu’a kan kowane irin barna da bala’o’i da ke faruwa a jihar, Malamai sun kuma nemi tsarin Allah, ya kuma yi masa ni’ima da rahamarsa da kuma dauwamammen zaman lafiya a fadin jihar.

 Sun kuma yi addu’ar Allah ya ba gwamnan karfi da ikon ci gaba da gudanar da ayyukan alheri na kawo sauyi a jihar da ya faro cikin kasa da kwanaki 100 a ofis.

 Taron addu'o'in na musamman ya samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban da suka hada da;  Kwamishinoni, Daraktoci, Manyan Ma’aikatan Gwamnati da sauran jama'a.

 Kwamishinonin da suka halarci taron sun hadar da;  Hon.  Yakubu Ahmed BK, Information, Hon.  Abubakar Jiika, Finance, Hon.  Abdullahi Umar Muslim, Ayyuka da Akanta Janar na Jiha, Alhaji Muhammad Aminu Zoramawa, Alhaji Kabir Sani Gaint, SA siyasa da mulki, Sagir Muhammad Haliru, babban sakataren yada labarai na Gwamna Ahmed Idris da dai sauransu.

Latsa nan ka kalli Hotuna

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN