DSS ta kafa sabon cibiyar hulda da jama'a DPRSC, ta yi babban nadi ga wani hazikin Darakta


 Hukumar DSS ta kafa cibiyar hulda da jama’a da dabarun sadarwa (DPRSC) tare da nada Dokta Peter Afunanya a matsayin Darakta na farko.

 Sanarwar da hukumar ta fitar ranar Laraba a Abuja ta ce kafa DPRSC na daga cikin kokarin da hukumar ta DSS ke yi na ci gaba da cudanya da ‘yan kasa da jama’a.

 Sanarwar ta ce, hukumar na kuma kara zurfafa gudanar da mulkin dimokaradiyya, gaskiya da rikon amana a cikin ayyukan ta.

 Ya ce Afunanya, tsohon jami’in hulda da jama’a na DSS, shi ne zai jagoranci hukumar a matsayin daraktan sa ido sannan kuma zai kasance mai kula da harkokin sadarwar jama’a na hukumar.

 Sanarwar ta ce nadin ya fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Satumba, inda ta kara da cewa hukumar ta DSS ta yabawa Darakta Janar na hukumar Alhaji Yusuf Magaji Bichi bisa shirin fadadawa da nada Afunanya domin ya jagoranci hukumar.

 Afunanya ya samu digirin digirgir (Ph.D) a fannin tsaro da dabarun bincike daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi da kuma digiri na biyu a fannin zaman lafiya da dabarun yaki daga Jami’ar Ilorin.

 Ya ce sabon daraktan ya samu digirin digirgir a fannin koyar da harshen turanci daga jami’ar Uyo bayan ya kammala karatu a jami’ar jihar Abia da ke Uturu da digiri na biyu a fannin Ingilishi.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN