Ta faru jama'a : Boka ya ce zai iya tayar da gawar Mawaki Mohbad da ya mutu, duba lamarin..


 Wani Boka da ya bayyana kansa a matsayin Oba Ewulomi ya yi ikirarin cewa zai iya tada mawaƙin Najeriya Marigayi Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

 Ku tuna cewa Mohbad ya mutu a ƙarƙashin yanayi mai cike da cece-kuce a ranar 12 ga Satumba, 2023, kuma an binne shi washegari.

 Daga baya ne aka tono gawarsa domin yin binciken gawa bayan da jama’a suka yi ta cece-kuce domin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin rasuwarsa kwatsam.

 An ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawarwaki bayan da aka gudanar da binciken gawar kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

 Yanzu, Boka Ewulomi ya bukaci samun damar ganin gawar mawakin, inda ya yi alkawarin ta da shi.

 Da yake magana a cikin cakuda Turanci da Yarbanci a cikin bidiyon da ke zagayawa akan shafin X, Bokan ya dage cewa "Mohbad na iya sake rayuwa har yanzu."

 Ya ce, “Alkwari Imole Mohbad zai iya sake rayuwa.  Ku ba ni dama ga gawarsa zan tashe shi".  Tabbas

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN