Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji daga arewa maso yamma sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara da sanyin safiyar yau Litinin.
Sojojin sun yi aiki ne da wani rahoton sirri kan sace wasu da ba a tantance adadinsu ba daga kauyen Kayan Boggo da ke karkashin karamar hukumar Bukkuyum a jihar Arewa maso Yamma.
Wata majiya mai karfi ta soji ta shaida wa gidan talabijin na Channels TV cewa sojojin sun tattara tare da kafa wani shinge a hanyar da za a iya bi na wadanda ake zargin.
A cewar majiyar, an yi artabu da bindiga wanda ya tilasta wa ‘yan fashin gudu tare da yin watsi da mutane 15 da suka sato yayin da aka kashe wasu da ba a tantance adadinsu ba.
An mika wadanda aka yi garkuwa da su ga hakimin Gwashi domin hada su da iyalansu.
Published by isyaku.com