Rahotanni sun bayyana cewa shugaban karamar hukumar Ijebu Ode a jihar Ogun, Babatunde Emilola-Gazal, ya gudu daga ofishinsa bayan da wasu mazauna garin suka ba shi wa’adin da ya lissafto bayanin yadda aka sarrafa kudaden da majalisar ta samu a karkashin sa a cikin shekaru biyu da suka wuce.
Daily trust ta ga wata sanarwa da ke neman a binciki kasafin kudin majalisar karkashin Emilola-Gazal, wanda kuma shi ne shugabannin kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) a jihar.
Wakilin Daily Trust a Abeokuta ya ruwaito cewa lamarin ya biyo bayan zargin karkatar da kason kudaden LG da ya yi wa Gwamna Dapo Abiodun a kwanakin baya.
Shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas, Wale Adedayo, ya zargi Abiodun da karkatar da kason kudaden da gwamnatin tarayya ta kayyade na kananan hukumomi 20 na jihar.
Kansilolin LG sun dakatar da Adedayo a makon da ya gabata sakamakon zargin da ya yi wa gwamnan.
Haka kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tsare shi har na tsawon kwanaki uku bisa zargin tada jijiyar wuya ga gwamnati.
Daily trust ta tuna cewa Emilola-Gazal ne ya jagoranci wasu shugabannin kansilolin zuwa ofishin Gwamna Abiodun inda suka yi sujjada don rokon gafara a madadin Adedayo.
Published by isyaku.com