Lantarki ya halaka barawon wayoyin wuta a cikin transfoma a jihar Neja


Wani mutum da ba a san ko wanene ba, wanda ake zargin barawo ne, ya mutu bayan wutan lantarki ya ja shi lokacin da yake kokarin satar wayoyin tiransfoma a cikin harabar gidan da’a ta jihar Neja da ke Minna.


 Wasu ma’aikatan kamfanin Printing ne suka gano gawar mutumin, tana rataye a kan taransfoma da sanyin safiyar Juma’a 8 ga Satumba, 2023.


 Shugaban Legal Unit na kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja, AEDC, Aminu Ubandoma, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.


 Ya ce kamfanin ya sha samun rahotanni da dama na lalata taranfoma.


 Ya bayyana cewa kamfanin yana aiki da jami’an tsaro musamman ‘yan sanda domin ganin an rage yawan barnatar da taransifoma zuwa mafi karanci.


 Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Juma’a, an samu rahoton wani lamari da ake zargin ya yi sanadiyar lalata wutar lantarki.


 Ya ce lamarin ya faru ne a kusa da tsohuwar unguwar sakatariyar da ke harabar ma’aikatan buga takardu inda aka tsinci gawar wani babba namiji da har yanzu ba a tantance ko waye ba a wata taransfoma da kebul da wayoyi da ya lalace su.


 Ana zargin wutar lantarki ce ta kama shi.


 Mista Abiodun ya ce tawagar ‘yan sintiri Morris ne suka kai gawar zuwa babban asibitin Minna kuma an tabbatar da mutuwarsa a asibitin.


 Ya kuma kara da cewa, ana ci gaba da kokarin gano dan uwan ​​marigayin, saboda ana binciken lamarin tare da hadin gwiwar AEDC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN