Shi kenan: Abba Gida-Gida ya dau aniyar aurar da 'yar TikTok Murja Kunya


Fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Kunya za ta amarce a auren zaurawa da za a gudanar nan ba da jimawa ba a jihar Kano. Legit Hausa ya wallafa.

Wannan na fitowa ne daga bakin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida yayin da yake jawabi, Aminiya ta ruwaito.

Da yake bayani a gidan gwamnatin Kano, Abba gida-Gida ya ce zai aurar da Murja a shirinsa na aurar da zaurawa da za a yi a jihar don raya sunnah.

A cewar Abba, aurar da Murja zai zama yi mata sakayya da irin gudunmawa da kokarin da ta yi wajen kafuwar gwamnatinsa a watan Maris din bana.

Ga dai abin da Abba ke cewa:

“Kowa ya san irin rawar da Murja ta taka wajen yayata ayyukan alheri da gwamnatin nan ke yi, wanda babu abin da za mu ce sai son barka.

“Kuma ita ce ta fara fitowa a cikin ’yan tawagarsu [’yan TikTok] ta ce tana son a yi mata aure sunnar Manzon Allah.
“Matar da ta fito ta ce tana son a inganta sunnah ta Manzon Allah ai ba a bar kyama bace.

“Kuma so take ta je inda za ta ba da gudunmawar inganta addinin Musulunci.”
Murja dai na daga cikin wadanda ke yawan jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta TikTok, inda kullum take cikin mayar da martani ga masu sukarta.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN