A ranar Alhamis ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kaduna ta tabbatar da zaben Sanata Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna.
Kotun ta yanke hukuncin ne a karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Isah Mohammed Ashiru suka shigar. PM News ya rahoto.
Ashiru ya kalubalanci nasarar Sani a zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga Maris, Kotun ta ce an zabi Sani bisa ka'ida.
Published by isyaku.com