Ya aikata: Tsoho mai shekara 70 ya taushe yarinya kurma yar shekara 13 ya yi mata fyade har ta mutu


An kama wani tsoho dan shekara 70 mai suna Anthony Mgbenwa Okpara da laifin yiwa wata yarinya kurma mai shekaru 13 fyade har lahira a jihar Enugu a kauyen Aborjieze da ke yankin Umuagu-Inyi mai cin gashin kansa a karamar hukumar Oji ranar 23 ga watan Satumba.

 A cewar mazauna yankin. Yarinyar mai suna Uche, ta rasu ne bayan da wanda ake zargin ya yi lalata da ita.

 "Gawar yarinyar tana cikin dakin ajiyar gawa yayin da muke magana kuma muna son a tantance wannan al'amari a cikin dokar da ta dace don zama kange ga sauran masu aikata laifuka," wata majiya ta shaida wa The Sun.

 Wanda ake zargin wanda aka kama bayan an kai rahoto ga ‘yan sanda, yanzu haka yana tsare a hedikwatar ‘yan sandan jihar Enugu.

 Mazauna unguwar sun ce sun kuduri aniyar ganin an yi wa yarinyar adalci  domin yarinyar kurma ce, kuma iyayenta na fama da talauci, saboda mai yiwuwa wanda ake zargin ya so ya yi amfani da kudi domin lalata lamarin kafin a kai shi gaban kotu.

Published by isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN