Da duminsa: An yi yunƙurin kifar da gwamnatin sojin Burkina Faso


 Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta daƙile yunƙurin yi mata juyin mulki, shekara guda bayan shugaban ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traore ya hau mulki ta hanyar hamɓarar da gwamnatin baya. Aminiya ta rahoto.

Gwamnatin Kyaftin Traore ta ce a ranar Talata wasu sojoji suka yi yunƙurin hamɓarar da ita, amma ta damke su.

Karo na biyu ke nan cikin mulkinsa na shekara guda da gwamnatinsa ta sanar da nasararta wajen daƙile yunƙurin kifar da ita.

Abin takaici sojojin da suka yi rantsuwa za su ƙare ƙasarsu sun ɗauki hanyar jefa ƙasar cikin bala’i,” in ji sanarwar gwamnatin ta gidan talabijin na ƙasar.

Bayan sanarwar da kira magoya bayan Traore su kare Burkina Faso ne dubban al’ummar ƙasar suka fito kan titunan birnin Ouagadougou a daren suna jaddada goyon baya gare shi.

Hukumar leken asirin kasar ta ce tana binciken sojojin da suka yunkurin juyin mulkin, tare da neman sauran masu hannu a ciki ruwa a kallo.

Wannan na zuwa ne bayan a watan hukumar ta sanar da cafke wasu sojoji da tsoffin ke aiki a ƙarƙashinta kan zargin tattara bayanai ta bayan fage da kuma bibiyar motsin Kyaftin Ibrahim Traore da manyan jami’an gwamnatimsa.

Wata takwas kafin nan, gwamnatin Traore ta sanar da daƙile yunƙurin kifar da ita a watan Disamban 2022, wata bayan ya yi nasa juyin mulkin.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN