Wani dan kasuwa, Ssaalongo Nsikonenne Habib Ssezzigu, ya auri mata bakwai a rana guda a kasar Uganda.
An yi bikin auren ne a ƙauyen Bugereka, a gundumar Mukono ranar Lahadi, 10 ga Satumba, 2023.
Biyu daga cikin mata bakwai da ya aura ’yan’uwan juna ne.
An fara gudanar da aikin ne da misalin karfe 8 na safe, inda aka kai Amaren dakin gyaran jiki domin yin salon gashi, kafin a sanya su a cikin motocin dakon kaya na Super Custom, dauke da faranti na musamman Wanda ke dauke da sunayen kowacce Amarya.
Bayan sun yi musabaha na aure, Nsikonnene da matansa guda bakwai sun gudanar da gagarumin jerin gwano karkashin jagorancin masu tuka keke babura da ake Kira "boda", suka bi ta garuruwan Kalagi, Kasana, da Nakifuma, kafin su isa gidansu da karfe shida na yamma.
An fara bikin daurin auren ne da kade-kade a yayin da ma'auratan ke tafiya a cikin ayarin motoci, yayin da jama'a suka yi dafifi a bakin titi domin shaida bikin.
Wasu mutane sun kasa gaskata cewa gaskiya ne wannan abu yana faruwa, wasu sun ce wannan shi ne karo na farko da za su halarci irin wannan taron daurin aure.
Matan sun hada da Mariam, Madina, Aisha, Zainabu, Fatuma, Rashida, da Musanyusa, wacce ita ce matar Habib ta farko kuma tana tare da shi tsawon shekaru bakwai.
Haka Habib ya siyo sabbin motocin a matsayin kyauta ga kowanne daga cikin matansa.
A wajen liyafar, an shirya kujerun angonta, kowanne da sunayensu.
Nsikonnene a jawabinsa a wajen liyafar, ya yabawa matansa bisa yadda suke yi masa biyayya.
Published by isyaku.com