Da duminsa: An kama Kwamishinan yan sanda na bogi, duba abin da biyo baya


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wani kwamishinan ‘yan sanda na bogi.


 Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a baya-bayan nan.


 Ya ce an kama wanda ake zargin “CP na jabu”, mai suna Emmanuel, a ranar 2 ga Satumba, da misalin karfe 4.40 na yamma.  a lokacin da ya ziyarci rundunar ‘yan sanda a yankin Ikorodu kuma ya gabatar da kansa a matsayin kwamishinan ‘yan sanda.


 "An martaba shi,  amma da aka tambaye shi, an gano shi kwamishinan jabu ne.  A yayin bincike a gidansa, mun gano katin shaidar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Kenwood walkie-talkie,  camouflage na ‘yan sanda, singlet da hular fuska na yan sanda,” inji shi.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN