Babbar magana: Wata mata ta zane Alkali da bulala, duba dalili


Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Abakaliki, Jihar Ebonyi, ta tasa keyar wata mata mai shayarwa ‘yar shekara 32, Misis Ann Akpa bisa zargin cin zarafin wani Alkali.


 ‘Yan sanda sun gurfanar da Akpan Ann a gaban kuliya bisa zarginta da yi wa majistare Lilian Igwesi bulala da sanda a ranar 28 ga watan Agusta 2023 a lamba 32 Hill Top Road, Abakaliki.


 Wanda ake tuhuma a cikin karar tuhuma biyu mai lamba MAB / 630c/2023 an kuma zarge ta da haddasa rashin zaman lafiya ta hanyar zuba datti a cikin gidan Majistare.


 Mai gabatar da kara na ‘yan sanda, ASP Chinagorom Eze, ta ce ta aikata laifukan da za a hukunta su a karkashin sashe na 335 da 249 (d) na kundin laifuffuka, Cap.  33, Juzu'i na 1, Dokokin Jihar Ebonyi, Nijeriya, 2009.


 Wanda ake tuhumar ta ki amsa laifuka biyun da ake tuhumarta da su na cin zarafi da haifar da rashin zaman lafiya.


 Lauyan wanda aka yi kara A. J. Uguru, Esq,  ya nemi a ba shi belin wanda ake kara, inda ya bayyana cewa laifin da ake tuhumata da su laifuka ne wanda ake iya bayar da beli.


Sai dai Alkalin kotun, Lynda Ogodo ta ki bayar da belin, ta kuma bayar da umarnin tsare ta a gidan yari na Abakaliki, sannan ta dage zaman Kotun zuwa ranar 27 ga watan Satumban 2023.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN