Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro cewa maharan kimanin mutane shida sun kutsa gidajen wasu bayin Allah a Unguwar Makabarta shiyar Polwaya suka dauke mutane biyu cikin dare.
Kazalika shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa da karfe 1:40 na dare, maharan sun ketara gidan wani mai suna Bashar inda suka yi artabu kuma suka raunata shi ta hanyar sara da adduna da kuma duka da sanduna.
Majiyarmu ta ce an garzaya da Bashar zuwa asibitin garin Koko, daga bisani aka zarce da shi zuwa asibitin tarayya na Federal Medical Center a garin Birnin kebbi don samun kulawa.
Sai dai bayanai na cewa maharan sun dauke wasu mutane biyu da suka hada da Nura Dan Umma Magaji da Faruku Dan Tabuda. Maharan sun kira lambar waya ranar Talata 19, Satumba suna bukatar a biya Naira miliyan 15 kudin fansa.
Majiyarmu ta ce an sanar da Yan sanda kuma sun fara bincike.
Sai dai bayan tuntubar Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi da muka yi kan lamarin, har lokacin rubuta wannan rahotu bamu sami martani ba.
Published by isyaku.com